A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Shugaban Makarantun Ilimin Addinin Musulunci na Iran, Ayatullah Alireza A’arafi, ya fitar da wata sanarwa mai zurfin nazari da dabarun tunkarar yanayi, a farkon mako na 12 na abin da ya kira yaƙin tilastawa na uku. A cikin sanarwar, ya bayyana muhimman nauyin da ke kan jami’an gwamnati, malamai da al’umma, tare da jaddada cewa duk wani ja da baya daga mashigar Hormuz yana nufin mika makullin tattalin arziki da tsaron Iran ga maƙiyi.
Ga fassarar cikakkiyar sanarwar:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Allah Maɗaukaki yana cewa:
إِنَّ الَّذِینَ قَالُوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ اسْتَقَامُوا تَتَنَزَّلُ عَلَیْهِمُ الْمَلَائِکَةُ أَلَّا تَخَافُوا وَلَا تَحْزَنُوا وَأَبْشِرُوا بِالْجَنَّةِ الَّتِی کُنْتُمْ تُوعَدُونَ
Ma’ana: "Lallai waɗanda suka ce Ubangijinmu shi ne Allah, sannan suka tsaya kyam a kan wannan, mala’iku za su riƙa sauka a kansu suna cewa: Kada ku ji tsoro, kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljannar da aka yi muku alƙawari."
Mun shiga mako na goma sha biyu na yaƙin tilastawa na uku, a daidai lokacin da maƙiya, Amurka da Isra’ila, mai girman kai da kashe yara, bayan shan kaye a fagen yaƙi da diflomasiyya, da kuma gazawarsu wajen buɗe mashigar Hormuz ta hanyar killace ta ta ruwa, ya ƙaddamar da wani samame da ya kira da sunan Aikin 'Yanci.
Sai dai, da taimakon Allah, tun daga farkon wannan yunƙuri, dakarun sojinmu sun mayar masa da martani mai ƙarfi, wanda ya tilasta masa ja da baya. A halin yanzu, kamar yadda yake a da kafin wannan samame, ikon gudanarwa da kula da mashigar Hormuz yana hannun dakarun sojin ƙasa da na Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), waɗanda suke da jarumta da sadaukarwa.
Rufe mashigar Hormuz a haƙiƙanin gaskiya yana nufin toshe muhimmin hanyar tattalin arzikin ƙasashen Yamma da Amurka. Ƙoƙarin Amurka na sake buɗe wannan mashiga kuwa har yanzu bai haifar mata da sakamakon da take so ba.
A wannan yanayi, Trump, mai aikata laifuffuka, ba shi da wasu hanyoyi fiye da guda uku:
Na farko: Ya amince da dukkan sharuɗɗan Iran, sannan ya sanar da shan kaye a wannan yaƙi. Wannan kuwa yana nufin rugujewar matsayinsa da kuma rasa matsayin Amurka na babbar ƙasa mai iko a duniya.
Na biyu: Ya yi ƙoƙarin samun wasu rangwame ta hanyoyi daban-daban a fagen diflomasiyya da tattaunawa.
Na uku: Ya kai wasu hare-haren soji kan muhimman ababen more rayuwar Iran, ya kunna ayyukan ƙungiyoyin adawa na cikin gida da na ƙasashen waje, sannan ya sanar da kawo ƙarshen yaƙin. Bayan haka, ya yi amfani da gagarumin yaƙin yaɗa labarai domin tabbatar da labarin nasarar da yake son jama’a su yarda da shi, ta haka ya fita daga wannan mawuyacin hali.
Babu shakka, al’ummar Iran, jami’an gwamnati, dakarun soji da kuma Ƙungiyoyin Gwagwarmaya (Axis of Resistance), ƙarƙashin jagorancin Jagora Sayyid Mujtaba Khamenei (Allah Ya ƙara masa ɗaukaka), za su ci gaba da jihadi da gwagwarmaya cikin haɗin kai da haɗin gwiwa. Haka kuma, suna shirye domin fuskantar duk wani yanayi da zai iya tasowa a nan gaba. Da dogaro ga Allah da neman taimakonsa, za su wargaza makircin maƙiya.
Maƙiya, Amurka da Isra’ila, wanda suka yi zaton za su iya cimma munanan manufofinsu cikin ’yan kwanaki, bayan shafe makonni goma da fara wannan yaƙi, ba wai kawai sun gaza cimma waɗannan manufofi ba ne, har ma sun tsinci kansu cikin wani babban mawuyacin hali a zurfin dabarun Iran na “dakile maƙiyi ta hanyar ɗaukar mataki mai tasiri”. Yanzu yana kallon yadda Iran ke gudanar da gwagwarmaya da juriya ta tarihi, tare da samun nasarorin da suka ba ta daraja.
Muna godiya ga Allah Maɗaukaki bisa babbar ni’imar haɗin kai, haɗin gwiwa, jihadi da kuma gwagwarmaya ta musamman da al’ummar Iran, jami’an gwamnati da dakarun sojin ƙasar suka nuna.
Domin ci gaba da wannan hanya mai albarka da kuma nuna godiya ta aikace ga wannan babbar ni’ima, wajibi ne manyan malamai, cibiyoyin Hauza, cibiyoyin wa’azi da al’adu, da kuma ƙwararru da masana a Hauza da jami’o’i su ci gaba da kasancewa a sahun gaba kamar yadda suka yi a yaƙe-yaƙen baya da kuma wannan yaƙi.
Bugu da ƙari, ya kamata su ci gaba da inganta kasancewarsu a fagen aiki da jihadin wayar da kan al’umma, bisa waɗannan dabaru:
1. Ƙarfafa fata da haɗin kai, da kuma ƙudurin jihadi da gwagwarmaya a tsakanin al’umma ta hanyar wayar da kai
Maƙiya, Amurka da Isra’ila suna ƙoƙarin tilastawa Iran ja da baya a hankali. Da farko a fagen yaƙi, daga nan a diflomasiyya, sannan a tattalin arziki, daga ƙarshe kuma a tunani da ƙudurin al’umma.
Ja da baya ko yi wa kafirai biyayya, ko da da taku guda ne, shi ne farkon faɗuwa da shan kaye, kuma ya saɓa wa umarnin Alƙur’ani a sarari. Allah Maɗaukaki yana umartar Annabinsa da cewa:
یَا أَیُّهَا النَّبِیُّ اتَّقِ اللَّهَ وَ لَا تُطِعِ الْکَافِرِینَ وَ الْمُنَافِقِینَ
Ma’ana: Ya kai Annabi! Ka ji tsoron Allah, kada ka bi kafirai da munafukai. (Suratul Ahzab: 1)
Haka kuma, wannan ya saɓa wa shawarar da Jagoranmu Shahidi ya sha jaddadawa, yana mai dogaro da wannan aya:
فَلَا تُطِعِ الْکَافِرِینَ وَجَاهِدْهُمْ بِهِ جِهَادًا کَبِیرًا
Ma’ana: "Kada ka bi kafirai, kuma ka yi musu jihadi da Alƙur’ani, jihadi mai girma." (Suratul Furƙan: 52)
Wannan shi ne abin da ake kira da Jihadi Mai Girma (Jihadul Kabir).
Alƙur’ani Mai Girma ya yi magana kan waɗanda suke kira zuwa ga yin sulhu ko sassauci daga rauni, ko kuma miƙa wuya ga buƙatun maƙiyi saboda jahilci, tsoro, kutsen maƙiya ko rashin yarda da alƙawuran Allah, inda yake cewa:
فَلَا تَهِنُوا وَ تَدْعُوا إِلَى السَّلْمِ وَ أَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ
Ma’ana: "Kada ku yi rauni, kada ku kira zuwa ga sulhu na wulaƙanci alhali kuwa ku ne kuke da fifiko." (Suratul Muhammad: 35)
Allah Maɗaukaki ya kuma ba wa muminai darasin juriya wanda zai ci gaba da kasancewa har ƙarshen duniya a cikin aya ta 156 ta Suratu Ali Imran:
وَ کَأَیِّنْ مِنْ نَبِیٍّ قَاتَلَ مَعَهُ رِبِّیُّونَ کَثِیرٌ فَمَا وَهَنُوا لِمَا أَصَابَهُمْ فِی سَبِیلِ اللَّهِ وَ مَا ضَعُفُوا وَ مَا اسْتَکَانُوا...
Ma’ana: "Da yawa daga cikin Annabawa ne suka yi yaƙi tare da mabiyansu masu yawa, amma ba su karaya ba saboda abin da ya same su a tafarkin Allah, ba su yi rauni ba, kuma ba su miƙa wuya ba."
Waɗannan siffofi guda uku, wato karaya, rauni da miƙa wuya, su ne ainihin abubuwan da maƙiyi yake son haifarwa a cikin sahun al’umma a yau.
Yana ƙoƙarin gajiyar da mu ta hanyar matsin lamba na tunani, raunana mu ta hanyar takunkumin tattalin arziki, sannan ya kai mu ga miƙa wuya da karɓar wulaƙanci ta hanyar barazanar kai hare-haren soji.
Alhali kuwa Alƙur’ani Mai Girma ya bayar da umarni bayyananne, wanda ba shi da wani keɓancewa, inda yake cewa:
وَ لَا تَهِنُوا وَ لَا تَحْزَنُوا وَ أَنْتُمُ الْأَعْلَوْنَ إِنْ کُنْتُمْ مُؤْمِنِینَ
Ma’ana: "Kada ku karaya, kada ku yi baƙin ciki, domin ku ne kuke da fifiko idan kun kasance muminai." (Suratul Ali-Imran, 132)
Ya kamata a lura cewa a wannan fafatawa, maƙiyi ya fi mu samun asara da rauni. Wannan kuwa a daidai lokacin da maƙiyi ba ya da fatan samun taimakon Allah, alhali Allah Ya yi wa muminai alƙawarin taimakonsa.
Alƙur’ani yana cewa:
وَلَا تَهِنُوا فِی ابْتِغَاءِ الْقَوْمِ إِنْ تَکُونُوا تَأْلَمُونَ فَإِنَّهُمْ یَأْلَمُونَ کَمَا تَأْلَمُونَ وَتَرْجُونَ مِنَ اللَّهِ مَا لَا یَرْجُونَ وَکَانَ اللَّهُ عَلِیمًا حَکِیمًا
Ma’ana: "Kada ku yi rauni wajen neman maƙiya. Idan kuna jin raɗaɗi, to su ma suna jin raɗaɗi kamar yadda kuke ji. Amma ku kuna fatan samun abin da ba sa fata daga Allah. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima." (Suratul Nisa'i: 104)
Bisa ga labarai da rahotanni, a halin yanzu akwai matsin tattalin arziki mai tsanani a ƙasashen Yamma, musamman Amurka, wanda ya sanya ’yan siyasa da masu son yaƙi a cikin al’ummar Amurka fuskantar matsin lamba da matsaloli.
Saboda haka, ɓangaren da zai nuna ƙarancin juriya shi ne zai sha kaye a wannan fafatawa.
Wajibi ne a kan dukkan ɗaliban Hauza da malamai su yi amfani da dukkan ƙarfinsu wajen ƙarfafa fata, haɗin kai da ƙudurin jihadi da gwagwarmaya a cikin al’umma ta hanyar wayar da kai.
A wannan fafatawa da maƙiyi yake son raunana ƙudurin al’ummarmu ta hanyar yaɗa shakku, barazana da matsin tattalin arziki, ku waɗanda kuka gaji aikin Annabawa, ya kamata ku yi amfani da ayoyin Alƙur’ani da jihadin wayar da kai wajen wargaza makircin maƙiyi da ƙarfafa sahun muminai.
2. Bayyana muhimmancin diflomasiyya mai 'yanci da basira, neman tabbatar da ita da kuma faɗaɗa diflomasiyyar Musulunci da juyin juya hali
Dabara ta biyu ita ce bayyana muhimmancin diflomasiyya mai 'yanci da kuma wayar da kan al’umma domin neman tabbatar da ita.
Wajibi ne a kasance cikin lura da makircin maƙiyi na tsagaita wuta ta yaudara.
Bayan shafe kusan kwanaki 80 suna shan kaye a fagen fafatawa, Amurka da masu goyon bayanta za su yi ƙoƙarin jawo yaƙin zuwa teburin tattaunawa, domin su samu abin da suka kasa cimmawa ta hanyar hare-haren soji, ta amfani da alkawura masu ƙayatarwa amma na ƙarya.
Ya kamata a lura cewa duk wata diflomasiyya a wannan yanayi dole ne ta dogara da ginshiƙai guda biyu:
1. Ƙarfi da ɗaukaka.
2. Tabbatar da nasarorin da aka samu a fagen fafatawa.
Mafi muhimmancin waɗannan nasarori shi ne ci gaba da riƙe cikakken iko da kula da mashigar Hormuz a hannun dakarun sojin Iran.
Mashigar Hormuz ba kawai hanyar ruwa ta ƙasa da ƙasa ba ce, ita ce muhimmiyar jijiyar tsaron ƙasa da tattalin arzikin Iran, kuma tana cikin manyan iyakokin da ba za a yarda a ƙetare su ba. Duk wani ja da baya a wannan batu yana daidai da mika makullin tattalin arziki da tsaron Iran ga maƙiyi.
Dole ne a bayyana a sarari cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin cikakken iko da gudanarwar dakarun sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babu wani jami’in ƙasar waje ko wata yarjejeniya ta yaudara da za ta iya ba da damar ƙetare wannan jan layi.
A yunƙurinsa na ƙarshe na rashin nasara, shugaban Amurka mai rauni da ruɗani ya sanar da wani shiri mai suna Shirin 'Yanci, domin buɗe mashigar Hormuz ta amfani da ƙarfi da ƙarfin soji, tare da hana dakarun Iran ci gaba da kula da mashigar.
Sai dai cikin ƙasa da sa'o'i 48, ya ja da baya daga wannan shiri bayan shan kaye mai girma da wulaƙanci.
Wannan yunƙuri da bai yi nasara ba, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka suka bayyana, ya fallasa iyakokin ƙarfinta da raunin da take da shi wajen tilasta wani sabon yanayi a mashigar Hormuz, wadda take ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri ta ruwa a duniya.
Saboda haka, wajibi ne a kiyaye wannan babbar dama ta dabarun ƙasa da ƙasa da Iran take da ita ta hanya mafi inganci.
Ya kamata al’umma, ɗaliban Hauza da malamai su bayyana wannan gaskiya da murya bayyananniya:
- Ja da baya a gaban matsin lambar maƙiyi shi ne farkon faɗuwa da ja da baya a kai a kai. Ɗaukaka, mutunci da kimar al’ummar Iran ba za su bari ta amince da sulhun da aka tilasta mata ko miƙa wuya saboda barazana da wulaƙanci ba.
- Tsayin daka wajen kula da mashigar Hormuz, wanda yake daga cikin buƙatun Jagoran juyin juya halin Musulunci a saƙonninsa, shi ne babban shinge ga kwaɗayin maƙiyi.
- Babu wata tattaunawa da za a amince da ita idan tana yin watsi da nasarorin da aka samu a fagen fafatawa ko kuma tana son sauya tsarin kariya da tsaron Iran.
Diflomasiyyarmu dole ne ta kasance mai 'yanci da basira. Ɗaukaka kuwa tana cikin tabbatar da abubuwan da aka cimma ta hanyar jinin Shahidin Jagora da matasan wannan ƙasa.
Tare da jaddada muhimmancin diflomasiyya mai basira wadda za ta kawo mafita, da kuma yaba wa hukumomin da abin ya shafa, muna kuma jaddada buƙatar faɗaɗa hulɗar ƙasa da ƙasa, ƙarfafa dangantaka da abokan juyin juya halin Musulunci da gwamnatocin da ke tare da shi, da kuma faɗaɗa diflomasiyyar jama'a da al'adu tare da amfani da manyan damar da juyin juya halin Musulunci yake da su.
3. Taimakawa wajen inganta tattalin arzikin ƙasa da kuma rayuwar al’umma
A halin yanzu, ƙasar tana fuskantar matsalolin tattalin arziki daban-daban, kuma hauhawar farashi marar ƙa'ida ta sanya rayuwa ta yi wuya ga masu matsakaicin ƙarfi da kuma masu ƙaramin ƙarfi.
Wannan mummunan yanayin tattalin arziki yana da manyan dalilai guda uku:
Dalili na farko: Manufofin tattalin arziki da aka gina bisa tunanin tsarin jari-hujja, waɗanda aka aiwatar, tare da wasu kurakurai da gazawa. Waɗannan su ne suka haifar da matsaloli da rikice-rikice a ƙasar.
Dalili na biyu: Maƙiyan ƙasashen waje, takunkuman tattalin arziki na zalunci da kuma yaƙin da aka ɗora wa ƙasar ta fannoni daban-daban.
Dalili na uku: Masu son duniya da masu neman riba ta haram a cikin gida, waɗanda suke taimakawa maƙiyi wajen cimma manufofinsa ta hanyar ɓoye kayayyaki da ƙara farashinsu ba bisa ƙa'ida ba.
A cikin wannan yaƙi mai haɗa hanyoyi daban-daban, maƙiyi yana ƙoƙarin ɗora wa al’umma matsin rayuwa da ƙara musu tsadar rayuwa, domin ya sa amincewa da sulhu da miƙa wuya ga buƙatunsa su zama kamar mafita. Haka kuma yana son sauya tunanin jami’an gwamnati domin cimma manufofin da ya kasa cimmawa ta hanyar yaƙi.
A wannan yanayi, malamai suna da muhimman ayyuka guda shida:
Na farko: Bayyana da yaɗa al’adar jihadin tattalin arziki.
Babban fagen jihadi a yau shi ne jihadin tattalin arziki. Ana iya cimma hakan ta hanyar ƙara ƙoƙari da aiki, inganta ingancin aiki da kuma bunƙasa samar da kayayyaki.
Na biyu: Shawartar al’umma da yin haƙuri, juriya da ƙarfafa fata.
Ya kamata a tunatar da al’umma cewa samun taimakon Allah yana da alaƙa da haƙuri da juriya irin ta muminai a lokacin wahalhalu da ƙalubale. Wannan kuwa wata ƙa’ida ce ta Allah wadda ba ta canzawa.
Allah Maɗaukaki yana cewa:
فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ یُسْرًا
Ma’ana: "Lallai tare da tsanani akwai sauƙi." (Suratul Inshirah: 4)
Haka kuma Ya ce:
وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا لَا یَضُرُّکُمْ کَیْدُهُمْ شَیْئًا
Ma’ana: "Idan kuka yi haƙuri kuma kuka ji tsoron Allah, makircinsu ba zai cutar da ku da komai ba." (Suratul Ali-Imran: 120)
Manzon Allah (S) ya kuma ce:
اَلصَّبْرُ مِفْتاحُ الْفَرَجِ
Ma’ana: Haƙuri shi ne mabuɗin samun mafita.
Na uku: Shawartar al’umma da guje wa almubazzaranci da yin amfani da abubuwa cikin tsari.
A yanayin yaƙi, almubazzaranci bai dace da mumini ba.
Ya kamata a jaddadawa al’umma cewa guje wa almubazzaranci, rayuwa cikin sauƙi, tallafawa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida da kuma amfani da su, duk waɗannan hanyoyi ne na kawo cikas ga yaƙin tattalin arziki na maƙiyi da kuma wargaza makircinsa.
Haka kuma, ya kamata kowa ya aiwatar da shawarwarin jami’an gwamnati da masu gudanar da shirye-shirye kan yin tanadi da rage ɓarnar amfani da makamashi, ruwa, wutar lantarki da iskar gas.
Na huɗu: Ƙarfafa sa ido na jama’a domin gano masu cin hanci da rashawa a tattalin arziki, masu ɓoye kayayyaki da masu tsawwala farashi.
Ba ya halatta a yi shiru a kan tsawwala farashi, ɓoye kayayyaki da cin hanci da rashawa a tattalin arziki.
Ya kamata ɗaliban Hauza su roƙi al’umma da su kasance cikin lura, su taimakawa hukumomin da abin ya shafa wajen gano masu cin hanci da rashawa, masu ɓoye kayayyaki da kuma masu tsawwala farashi a wannan mawuyacin lokaci.
Na biyar: Samar da buƙatar jama’a ta aiwatar da tsarin tattalin arziki mai juriya (Resistance Economy).
Bisa la’akari da cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sanya sunan wannan shekara da Shekarar Tattalin Arziki Mai Juriya, a Inuwar Haɗin Kan Ƙasa da Tsaron Ƙasa, wajibi ne malamai su mayar da aiwatar da tsarin tattalin arziki mai juriya ya zama buƙatar jama’a ga hukumomin tattalin arziki na gwamnati, Majalisa da bangaren shari’a.
Haka kuma, su nemi a tsara manufofin tattalin arziki bisa ƙa’idojin wannan tsari, a guji aiwatar da tsarin tattalin arzikin jari-hujja da tsarin tattalin arzikin da ya dace da yanayin zaman lafiya na yau da kullum, sannan a yaƙi masu cin hanci da rashawa da gaske.
Ya kamata a nemi hukumomin tattalin arziki da su karkata manufofinsu zuwa ga tabbatar da adalci, tallafawa masu ƙaramin ƙarfi, ƙara darajar kuɗin ƙasa da kuma yaƙi da tsadar rayuwa, ɓoye kayayyaki da hauhawar farashi.
Na shida: Faɗaɗa al’adar taimakon juna da tausaya wa juna.
Jagoranmu Shahidi a jawabansa daban-daban, da kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci na yanzu a saƙonninsa na baya-bayan nan, sun bayyana yaɗa al’adar taimakon juna da tausayawa juna a tsakanin jama’a a matsayin muhimmiyar hanya ta magance matsalolin rayuwa da rage wahalhalu da raɗaɗin da al’umma ke fuskanta.
Saboda haka, wajibi ne malamai su ƙara faɗaɗa wannan al’ada ta taimakon juna da tausayawa juna a wannan mawuyacin lokaci.
4. Ba wa al’amuran al’adu muhimmanci da kuma taka-tsantsan wajen fuskantar yaƙin al’adu na tunani
Maƙiyan Amurka da Isra’ila sun yi zaton cewa ta hanyar kashe Jagoran juyin juya halin Musulunci, kwamandojin soji da fararen hula marasa laifi, al’ummar Iran za ta wargaje daga cikin gida, sannan tsarin mulkin ƙasar zai rushe.
Sai dai abin da ya faru a zahiri shi ne wata babbar mu’ujiza ta haɗin kai tsakanin sassa daban-daban na al’umma.
Wannan ya kai matsayin da Jagoran juyin juya halin Musulunci na yanzu ya bayyana al’umma a cikin saƙonsa a matsayin magaji nagari kuma wanda ya maye gurbin Jagoranci a lokacin rashin Jagoran al’umma da kuma shahadarsa.
Saboda haka, a bayyane yake cewa maƙiyi mai ƙiyayya yana ƙoƙarin kai hari da lalata wannan babbar makami mai matuƙar muhimmanci, wato haɗin kai da haɗin gwiwar ƙasa.
Ɗaya daga cikin batutuwan da babbar kafar yaɗa labaran maƙiyi take mayar da hankali a kai shi ne haifar da rarrabuwar kai a cikin al’umma ta hanyar amfani da batutuwa daban-daban, musamman batun Hijabi.
Tabbas, kamar yadda Jagoranmu Shahidi ya sha bayyana, sanya Hijabi wajibi ne kuma buƙata ce ta addini. Barin sa kuwa haramun ne ta fuskar shari’a da siyasa. Haka kuma, aikin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, bisa sharuɗɗan da Shari’a ta gindaya, yana cikin muhimman wajibai kuma yana tabbatar da farin cikin duniya da lahira.
Saboda haka, muna ba al’umma, jami’an al’adu, ɗaliban Hauza da malamai a duk faɗin ƙasar shawara mai ƙarfi da su yi amfani da wannan dama ta musamman wajen kusantar da wannan ɓangare na ’yan mata da mata, ta hanyar wayar da kai, ƙauna da girmamawa.
Haka kuma, su yi amfani da hanyoyi marasa tayar da husuma kai tsaye, kamar:
- Samar da ingantattun abubuwan ilmantarwa da za su yi tasiri a fagen Hijabi da kamun kai.
- Bayyana jarumai mata masu Hijabi, kamar iyaye mata da ’ya’ya mata masu gwagwarmaya a bayan fagen yaƙi.
- Bayyana matan da suka yi shahada a fagen fafatawa.
- Amfani da hanyoyi daban-daban na nasiha da tunatarwa ta baki, cikin kyakkyawar mu’amala da jan hankali.
Ta haka ne za a iya jagorantar yanayin zamantakewa da fagen al’adu a cikin al’umma.
Kada a bari wannan batu ya koma gardama mai tayar da hankali a tituna da unguwanni, ya zama sanadin rarrabuwar kai da rabuwar al’umma, ko kuma abin da kafafen yaɗa labaran da ke adawa da ƙasar za su yi amfani da shi. Haka kuma, kada a bari a yi watsi da aikin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.
5. Jaddada buƙatar cikakken jihadin al’umma da jami’an gwamnati
A lokacin tsagaita wuta da bayan yaƙi, akwai buƙatar sake gina wuraren da suka lalace, gyara abubuwan da suka lalace, bunƙasa ƙasa da kuma shawo kan matsaloli ta hanyar cikakken ƙoƙari da himma irin ta masu jihadi.
Saboda haka, cikakken jihadi da ƙoƙarin al’umma, jami’an gwamnati da masana a fannonin tattalin arziki, masana’antu, noma, ilimi, fasaha, soja, tsaro, masana’antun kariya, kariyar da ba ta hanyar makamai ba da sauran fannoni, wajibi ne na addini da na ƙasa wanda ya rataya a wuyan kowa.
Hukumomin ilimi da al’adu, Makarantun Ilimin Addinin Musulunci da kuma manyan shugabanni suna da alhakin tsara wannan yunƙuri, shiga cikinsa, haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki, neman aiwatar da shi da kuma wayar da kan al’umma game da muhimmancinsa.
6. Faɗaɗa al’adar Mahdawiyya da jiran bayyanar Imam Mahdi (AF), tare da shirye-shiryen karɓar bayyanar Babban Hasken Wilaya
A yau, jihadi da gwagwarmaya wajen fuskantar masu danniya a duniya, musamman Amurka mai aikata laifuffuka, ba kawai wata dabara ce ta ɗan lokaci ba. A’a, wani mataki ne na samar da wayewar kai ta kafin bayyanar Imam Mahdi (AF) da kuma share fagen tabbatar da alƙawarin Allah:
وَعَدَ اللَّهُ الَّذِینَ آمَنُوا مِنکُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَیَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِی الْأَرْضِ
Ma’ana: "Allah Ya yi wa waɗanda suka yi imani daga cikinku kuma suka aikata ayyukan ƙwarai alƙawarin cewa lallai zai sanya su magada a cikin ƙasa."
Haka kuma, wannan gwagwarmaya wani horo ne na shirya kai domin samun damar rayuwa ƙarƙashin gwamnatin duniya baki ɗaya ta Imam Mahdi (AF).
A yau, Amurka ita ce misalin Ɗagutu na ƙarshen zamani da kuma Sufyanin zamani. Gwagwarmaya da ita kuwa yana nufin yaƙi da mataimaka da magoya bayan Dajjal na wannan zamani, da kuma tsayawa a sahun mataimakan Imam Qa’im (AF) tun kafin bayyanarsa. Haka kuma, wannan gwagwarmaya horo ne na koyon jarumta, ikhlasi da biyayya ga Jagoranci, waɗanda suke daga cikin fitattun siffofin mataimakan Imam Mahdi (AF).
Imam Ja’afar Sadik (AS) yana cewa: "Duk wanda ya shirya kansa domin taimakon Imam Qa’im ɗinmu, ko da da kibiya guda ce, yana kama da wanda ya yi yaƙi a ƙarƙashin tutarsa."
Ana sa ran dukkan ɗaliban Hauza da malamai masu jihadi a yau su kasance a sahun gaba a fagen jihadi da gwagwarmaya, wajen faɗaɗa al’adar Mahdawiyya da jiran bayyanar Imam Mahdi (AF).
Ya kamata su bayyana wa al’umma cewa yaƙin da muke yi a yau yaƙi ne da kafirci, munafunci, Ɗagutu da rashin adalci. Ta hanyar jihadi, gwagwarmaya da samun nasara a wannan fafatawa ne za a share fagen bayyanar Imam Mahdi (AF).
Idan kuma aka nuna kasala da gazawa wajen wannan jihadi mai tsarki, aka ci nasara a kan sahun gaskiya, to za a mayar da shi baya, kuma za a ƙara nisa daga cimma manufofin Mahdawiyya da bayyanar Imam Mahdi (AF).
Muna fatan al’ummar Iran da kuma al’ummar Musulmi baki ɗaya za su sami wannan babban alfahari na share fagen bayyanar Babban Hasken Wilaya, kuma su sami dacewar yin jihadi a ƙarƙashin jagorancinsa.
وَمَا النَّصْرُ إِلَّا مِنْ عِنْدِ اللَّهِ الْعَزِیزِ الْحَکِیمِ
Ma’ana: Babu wani taimako da nasara face daga Allah, Mabuwayi, Mai hikima.
Ra'ayinka